Zabiya ya tsallake rijiya da baya a Tanzania

Image caption Masu larurar zabiya suna fuskantar kalubale a Tanzania

Wani zabiya ya tsallake rijiya da baya a kasar Tanzania bayan da wasu mutane suka nemi su kashe shi, a garin Mkuranga mai nisan kilomita 42 daga birnin Dar es Salaam.

Wasu mutane guda uku ne dai suka shiga gidan Muhammad Said mai shekaru 35 wanda kuma zabiya ne suka yi amfani da kyalle suka shake shi kafin daga bisani su sari gefen kansa da adda.

Sun kuma tafi sun bar shi a kwance suna tunanin ya mutu.

Al'amarin dai ya faru ne ranar Laraba duk kuwa a cewa sai a daren jiya Alhamis ne labarin ya fito fili.

Masu irin wannan larura dai suna fama da hare-hare a kasar ta Tanzania.