Majalisar dattawa ta tantance Amaechi

Hakkin mallakar hoto NTA

Majalisar dattawan Nigeria ta ci gaba da tantance mutanen da shugaba Muhammadu Buhari ya aike ma ta domin nada su a matsayin ministoci.

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi shi ne mutum na farko da ya bayyana gaban sanatoci a ranar Alhamis, inda ya bayyana ayyukan da ya yi a matsayinsa na tsohon gwamna.

Bayan shafe kusan awa daya ana yi masa tambayoyi, majalisar ta tantance shi aka ba shi damar ya rusuna wa sanatoci sannan ya tafi.

An dade ana cece-kuce kan Amaechi musamman saboda 'yan jam'iyyar PDP na adawa da shi.

Tun a makon jiya ne aka sa ran za a tantance Amaechi amma majalisar ba ta yi haka ba duk da cewar ta amince da mutane 18.

A zaman na ranar Alhamis, majalisar dattawan ta tantance Heineken Lokpobri daga jihar Bayelsa da Omoleye Daramola daga jihar Ondo da Baba Shehuri Mustapha daga jihar Borno da kuma Ocholi James daga jihar Kogi.