Kada na yin bacci da ido daya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kada yana barin ido daya a bude ne domin kare kansa daga duk wata barazana.

Wani sabon bincike da masana kimiyya a Australia suka gudanar ya nuna cewa kada yana bacci ne da ido daya sabanin yadda wasu halittu ke yi.

Binciken -- wanda aka wallafa a mujallar kimiyya Journal of Experimental Biology -- ya gano cewa kadoji suna yin bacci da bangaren kwakwalwa daya ne, suna barin daya bangaren yana lura da abubuwan da kan kai su komo.

Daya daga cikin masu binciken, John Lesku, ya ce kada yana horas da idonsa daya ne domin ya rika kula da barazanar da ka iya taso masa.

A cewar sa,"Kadoji suna lura da mutane a lokacin da suke cikin daki. Kuma ko da mutane sun fice daga dakin, kadoji suna ci gaba da barin ido daya a bude yana kallon wajen da mutanen suka bari domin shiryawa duk wata barazana da ka iya tasowa."

An gudanar da wannan bincike ne ta hanyar yin amfani da wata na'urar daukar hoto da ta sa ido kan yadda kadoji ke gudanar da rayuwarsu dare da rana.