Mace ta farko mai tuka jirgin sama a Nijar

Hakkin mallakar hoto State Gov
Image caption Ouma Laouali a daya daga cikin jiragen da za ta tuka

Laftanar Ouma Laouali ta zama mace ta farko a jamhuriyar Nijar da ta kasance mai tuka jirgin sama a rundunar sojin sama ta kasar.

'Yar shekaru 28, Ouma ta samu horo a Amurka da Afrika ta Kudu da kuma Morocco inda ta samu gogewa a tukin jirgin sama.

Za ta dinga tuka daya daga cikin jiragen saman da Amurka ta bai wa Nijar.

A ranar Laraba a birnin Yamai aka yi bikin mika wa Nijar jiragen saman kirar 'Cessna' domin yaki da ta'addanci.

Amurka ta yi wa Nijar alkawarin horas da sojoji da kuma samar da kayayyakin soji a wata yarjejeniyar tsaro da ta kai dala miliyan 24 a tsakanin kasashen biyu.

Hakkin mallakar hoto State.Gov

A yanzu haka, Amurka na da sansani a Yamai inda take da jirgi marar matuki guda daya sannan kuma za ta sake gina wani sansanin a Agadez duk a cikin dabarun da take amfani da su wajen yaki da ta'addanci a Afrika.