'Batun cin hanci a bangaren Man Nigeria'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Buhari ya sha alwashin murkushe cin hanci da rashawa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi mulki inda ya yi alkawarin magance matsalar cin hanci da rashawar da ya kewaye bangaren mai a kasar.

To ko zai iya magance wannan matsala?

Ko da yake ance kaso 75 cikin 100 na tattalin arzikin kasar daga bangaren mai ake samu, sai dai kuma babu wanda zai iya cewa ga iya abin da matatun man ke samarwa saboda a kowacce rana mutane na satar abin da suke sata daga bangaren man.

Shugaba Buhari ya karbi ragamar ma'aikatar man a wani yunkuri na rage cin hanci da rashawa.

Wasu kwararru hudu sun tattaunawa da BBC inda suka bukaci karin bayani a kan irin kalubalen da yake fuskanta.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bututan man Najeriya sun tsufa

Kolawole Banwo: 'Bayanai a kan satar mai da kuma ma'unin ma'aikatar man'

"Ba mu da wasu kayayyakin aikin da za mu iya auna yawan man da ake tace wa. Ba mu san ainihin iya hasarar da ake yi ba, amma a shekarar da ta gabata Najeriya na hasarar gangar mai dubu dari uku a kowacce rana, watau kusan dala biliyan 12 ke nan a shekara.

Dauda Garba: 'Mutane na bukatar cin gajiyar kudaden shigar da ake samu daga Mai'

"Idan mai shi ne hanyar samun kudin Najeriya, ba abin da za ayi da za a ce ya wuce ka'ida na ganin an gyara harkar.

"Muna bukatar mu sanya wata na'ura da za ta iya nuna man da ake debowa tun daga rijiyar man da kuma wuraren da ake tura man da ma inda ake loda su zuwa kasashen ketare."

Idayat Hassan:'Cin hanci da rashawa a Najeriya ya zama ruwan dare'

"Cin hanci da rashawa a Najeriya ya zama ruwan dare tabbas, saboda ya shafi ko ina a kasar. Zaka samu cin hanci a ko ina kai har ma a cikin harkokin yau da kulluma na al'ummar Najeriya akwai cin hanci".

"Idan ana gina asibitoci ko makarantu, to ko shakka babu masu wannan kwangila suna tafka abin da suka ga dama na cin hanci. Domin ba sa abin da yakamata".

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana sace dubban gangunan mai a kullum a Najeriya

Mansur Liman: Shin Buhari shi ne wanda zai iya warware matsala?

"Ina ga shi ne yakamata ya yi maganin abin da ke faruwa. Ga mutanen da suka san shi a lokacin da ya ke shugaban Najeriya na mulkin soja, sun san baya daukar wargi."

"A lokacin ne ya fito da wani abu da ake cewa 'yaki da rashin da'a'.Mutane basa bin tsaro amma Buhari ya sa dole kowa ya bi layi. Wanda ya soma zuwa shi ne za a fara yi wa abu."