Daliban Afrika ta Kudu na ci gaba da bore

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Dalibai sun ja daga da jami'an tsaro

Dalibai a Afirka ta Kudu na ci gaba da zanga-zangar adawa da karin kudin makaranta.

An shirya rufe daukacin jami'o'in kasar, kuma wani hoto da aka lika a shafukan sada zumunta na intanet ya nuna dalibai na taruwa a Jami'ar Pretoria, inda suke ta raye-raye da wake-wake.

Sakatare janar na kungiyar dalibai ta Afirka ta Kudu, Luzuko Buku, ya shaida wa BBC cewa " A matsayinmu na kungiyar daliban Afirka ta Kudu, mun ce daliban sun taka rawar gani sosai, amma akwai bukatar a kara kaimi saboda ba wani abu ne ya sa a ka yi biris da mu ba illa ganin ba a rufe jami'o'i ba."

Ranar Juma'a ake sa ran Shugaba Jacob Zuma zai gana da shugabannin jami'o'i da na dalibai a wani yunkuri na warware matsalar.