'Akwai yunwa a Sudan Ta Kudu'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yakin basasa a Sudan Ta Kudu ya janyo wa kasar yanayi na matsanancin yunwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban mutane ne ke fama da yunwa a kasar Sudan Ta Kudu.

Sashen kula da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ce za a iya shiga yanayi na yunwa a jihohin hadin gwiwa da ke kudancin kasar.

Kusan shekaru biyu bayan yakin basasar da ya yi sanadiyyar sanya mutane kusan miliyan hudu cikin matsanancin halin yunwa, sakamakon tarwatsa girbi na noma da tsadar abinci da na nan man fetur.

Iyalai da dama sun shiga wani hali na ha'ula'i, inda suke cin abinci so daya a rana, wanda bai wuci kifi ko fure ba.

Rashin jituwa tsakanin shugaban kasar, Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar ne ya janyo yakin.