Amurka ta soki Rasha a kan Assad

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Amurka ta ce bai kama Rasha ta tarbi Assad ba.

Gwamnatin Amurka ta soki kasar Rasha saboda ziyarar ba-zatan da shugaban Syria Bashar al-Assad ya kai birnin Moscow.

Wani kakakin gwamnatin Amurka ya soki Rasha saboda abin da ya kira yi wa Assad "tarba ta musamman".

Shugaban na Syria ya kai ziyarar ne ranar Talata makonni uku bayan Rasha ta kaddamar da hare-hare a kan 'yan kungiyar IS da ke ikirarin kishin Musulinci da sauran masu tayar da kayar baya a kasar ta Syria.

Wannan dai shi ne karon farko da Mr Assad ya kai ziyara wata kasa tun da yakin basasa ya barke a Syria a shekarar 2011.

Yakin yaki sanadiyar mutuwar a kalla mutane 250,000.