Al Shabaab ta yi mubaya'a ga IS

Image caption Al Shabaab ta dade tana kai hare-hare a Kenya.

Wani bangare da ya balle daga cikin kungiyar Al Shabaab da ke Somalia ya yi mubaya'a ga kungiyar IS da ke ikirarin kishin Musulinci.

Kungiyar, wacce ke da cibiya a yankin Galgala mai cike da tsaunuka a lardin Puntland, ta bayyana yin mubaya'ar ne a fili.

Kungiyar ba ta da girma a yanzu, kuma wani Malami mai suna Sheikh Abdiqadir Mumin ne ke jagorantar ta.

A kwanakin nan dai kungiyar IS ta fito fili tana neman mutanen da za su zama mambobin ta a Somalia, kuma ma tana amfani da kungiyar Boko Haram domin kara neman magoya baya.

Ita kan ta kungiyar Al Shabaab na da alaka da Al Qaeda, kuma shugabanninta sun sha samun sabani a kan 'yan kungiyar da ake zargi na shirin sauya ra'ayi.