Marubuta sun yi zanga-zanga a Indiya

Hakkin mallakar hoto PTI
Image caption Marubutan sun bukaci Narendra Modi ya dauki mataki.

Marubuta kimanin 100 ne suka yi zanga-zangar lumana a Delhi, babban birnin kasar Indiya domin, abin da suka ce, tsanar da ake ci gaba da nuna musu.

Marubutan sun mika wasika ga babbar makarantar nazarin adabi ta kasar, inda suka bukaci ta dauki matakin kare 'yancinsu.

A 'yan makonnin da suka gabata dai, marubuta 35 ne suka mayar da babbar kyautar da aka ba su a kan adabi domin bijirewa hare-haren da ake kai musu, ciki har da kisan da aka yi wa wani fitaccen marubuci.

Sun yi kira ga gwamnatin Firai Minista Narendra Modi da ta bayyana matsayinta kan halin da suke ciki.