Bom ya kashe mutane bakwai a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Garin Maiduguri da ke jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya ya sha fama da harin kunar bakin wake da ke da alaka da mayakan Boko Haram.

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na cewa, akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da aka kai da asubahin ranar Juma'a.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce, dan kunar bakin waken ya tayar da bam din ne a lokacin da jama'a ke sallar Asuba.

Babban jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta Nigeria NEMA a yankin arewa maso gabashin kasar Muhammad Kanar, ya shaida wa BBC cewa, an kwashe gawawwakin wadanda suka rasu, yayinda kuma aka kai wadanda suka jikkata asibiti.

Bayanai sun nuna cewa kimanin mutane 17 ne suka ji raunuka a harin, biyar daga cikinsu kuma sun samu munanan raunuka.

An dai kai harin ne a wani masallaci da ke bayan kotun majistare a Polon Maiduguri.

Karin bayani