APC ta kalubalanci PDP kan zaben Ribas

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike

A Najeriya, reshen jam'iyyar APC na jihar Ribas ya yaba da hukuncin da wata kotun shari'ar zabuka a kasar ta yi na soke zaben gwamnan jihar Nyesom Wike.

Jam'iyyar ta APC ta bakin shugabanta a jihar Ribas, Chief Devis Ebiyakun ya ce kamata ya yi jam'iyyar PDP ta rungumi kaddara, idan kuma ba haka ba, su na da damar kalubalantar hukuncin a kotun daukaka kara.

Reshen jam'iyyar PDP na jihar Ribas dai ya yi watsi da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke, wanda ya soke zaben gwamnan jihar na jam'iyyar, ya kuma bayar da umarnin a gudanar da wani sabon zabe nan da watanni uku.

Jam'iyyar PDP ta kara da cewa hukuncin da kotun ta yanke tamkar keta haddin tsaye ne ga Dimukradiyyar kasar.