Za a iya samun tsofaffin sakonni a Facebook

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Facebook yana son rike mabiya ka da su koma wata manhajar

Facebook ya dora tsofaffin sakonnin masu amfani da manhajar kimanin tiriliyan biyu, a kan shafin domin amfanin masu son yin waiwaye ga sakonni nasu.

Wannan tsarin dai yana nufin za a dawo da tsofaffin sakonnin da mutane suka sanya a shafikan nasu na Facebook.

Hakan yana nufin duk wanda yake neman wani bayani ko sako da ya taba wallafa wa a kan shafinsa na Facebook zai iya samun sa da zarar da ya nema.

Facebook ya bullo da wannan sabon tsarin ne domin tabbatar da cewa ma'abota shafin ba su bar manhajar ba zuwa wata a duk lokacin da suke neman bayanai.

Sai dai kuma mutanen da ba sa son wasu su ga bayanan da suka yi suna da zabi.

A yanzu haka dai masu mu'amila da Facebook a Amurka ne kadai suke cin gajiyar wannan tsari.

Ana ganin cewa tsarin da Facebook din ya fito da shi zai yi gogayya da manhajar sadarwa ta Twitter.

A baya-bayan nan ne shi ma Twitter ya kaddamar da wani sabon shafin na mahawara mai suna 'moments'.

Image caption Facebook ya fi Twitter yawan mabiya

Sai dai kuma Facebook yafi Twitter yawan mabiya nesa ba kusa ba.