An saka tsaro a Iraq saboda ranar Ashura

Image caption Yadda mabiya Shi'a ke dukan jikinsu ranar taron Ashura

An karfafa matakan tsaro a Iraki yayin da miliyoyin mutane suka taru don tunawa da ranar Ashura, daya daga cikin manyan tarukan addini na mabiya Shi'a.

Ana yawan kai hare-hare a duk lokacin da ake gudanar da wannan taro.

Miliyoyin mabiya Shi'a sun taru a birnin Kerbala da sauran muhimman wuraren addini saboda girmama ranar.

Mabiya Shi'a maza da mata sun sanya bakaken tufafi suna tafiya kan tituna suna sowa tare da dukan jikinsu.

Mabiya Shi'a dai suna wannan taro ne don tunawa da ranar da aka kashe Sayyadina Hussain jikan Manzon Allah SAW a shekara ta 680.