'Yar kunar bakin wake ta kashe mutane 3 a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto Screen Grab
Image caption Ana zargin kungiyar Boko Haram da kai hare-hare Maiduguri

Wata 'yar kunar bakin wake ta tayar da bam da ya yi sanadiyyar mutuwarta da wasu mutane uku a Maiduguri a ranar Asabar da safe.

Mutane da dama kuma sun jikkata sakamakon bam din da matar da tayar a unguwar Dala Yazaram da ke birnin.

Wani mazaunin unguwar ya ce ya ga mata biyu 'yan kunar bakin wake sun shigo unguwar wadda take da nisan kilomita shida daga cikin birnin Maiduguri, amma mutane sun dakatar da dayar yayin da dayar kuma ta yi maza ta tayar da bam din da ke jikinta.

Ko a ranar Juma'a ma mutane 28 ne suka mutu sakamakon wani hari da aka kai masallaci.

A baya-bayan nan dai Maiduguri na fama da ahre-haren da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suke kai wa.