Najeriya ta kamala jigilar alhazai zuwa gida

Wasu mahajjata 'yan Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu mahajjata 'yan Najeriya

Hukumar aikin hajji ta Najeriya ta ce ta kamala jigilar alhazan kasar zuwa gida , kwana hudu kafin wa'adin da aka debar mata ya zo karshe kuma kwanaki 7kafin a rufe filin saukar jiragen sama na sarki Abdulaziz da ke jedda.

A cikin wata sanarwa da shugaban hukumar Abdullahi Mukthar ya aikewa BBC ta ce wannan shi ne jigila mafi sauri a yan shekaru baya bayanan.

A baya Najeriya ta rika fuskantar matsala wajen jigilar alhazai zuwa kasa mai sarki ko dawo da su gida.

Sai dai 'yan Najeriya da dama suka rasa rayukansa a aikin hajjin ba ya yinda wasu suka ji raunuka a turmitsitsin da ya faru a ranar arafa da kuma fadowar kugiya mai daukar kaya mai nauyi.