Barclays ya fuskanci tangardar na'ura

Image caption Bankin ya ce an gyara tangardar

Bankin Barclays ya ce yana aiki domin gyara matsalar da ta kawo tsaiko ga masu mu'amila da bankin wajen shigar ko fitar da kudadensu.

Wasu dai sun kai wa bankin koken cewa an rufe musu katinansu na ATM a ranakun Asabar da Lahadi.

Mai magana da yawun bankin na Barclays ya shaida wa BBC ranar Lahadi cewa matsalar ta cikin gida ce.

Bankin ya fitar da wani sako ta hanyar shafinsa na Twitter da safiyar ranar Asabar cewa yana fuskantar matsalolin da na'urorinsa amma kuma ya ce ana bincike don gano a ina gizon yake saka.

A kuma wata sanarwa da bankin ya fitar ta kafar email ya ce " za mu iya tabbatar da cewa masu abokan huldatayyarmu suna ci gaba da amfani da bankin ba tare da matsala ba irin wadda suka fuskanta ranar Asabar, kuma muna neman afuwar abokan huldar tamu kan abin da ya faru".

Sai dai kuma wani abokin huldar bankin ya ce "duk da cewa an ta fadin cewa za a gyara matsalar ranar Asabar da misalin karfe biyar na yamma amma har safiyar Lahadi matsalar ba ta kau ba".

Image caption Amma masu huldatayya da bankin sun ce har yanzu matsalar ba ta gyaru ba

To amma mai magana da yawun bankin ya ce matsalar intanet ne ya hana masu huldatayya da bankin kasa cire ko ajiye kudadensu ba wai matsalar bankin ba ce. asu