Ana zabe a Tanzania da Ivory Coast

Image caption kasashen biyu suna zaben shugabannin kasa

A yau ne masu zabe a kasashen Tanzania da Ivory Coast suke fita rumfunan zabe domin zabar shugabannin kasashen.

A Tanzania dai za a fafata ne tsakanin gamayyar jam'iyyu da jam'iyya mai mulki ta CCM wanda take rike da ragamar mulkin kasar tun bayan samun 'yancin kai a shekarar 1961.

Za a kara ne tsakanin dan takarar jam'iyyar CCM mai mulki, John Magufili da tsohon piraiministan kasar Edward Lowassa wanda ya fice daga jam'iyyar ta CCM a baya-bayan nan.

A kasar Ivory Coast shugaban mai ci, Alassane Ouattara yana daya daga cikin 'yan takarar a inda yake neman sake koma wa kan mulkin kasar karo na biyu.

'yan takarar jam'iyyun adawa da dama sun fice daga jerin 'yan takarar dab da zaben, bisa zargin rashin sahihancin tsarin da aka bi wajen gudanar da shirye shiryen zaben.

Sakamakon babban zaben kasar ta Ivory Coast dai na shekarar 2010 ya jawo yakin basasa wanda da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu 3 sannan wasu da dama suka yi gudun hijra.

Hakan ya biyo bayan kin yarda da faduwa zaben da hambararren shugaban kasar, Laurent Gbagbo ya yi.