Girgizar kasa ta hallaka mutane 200

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Lamarin ya shafi kasashen India da Pakistan da kuma Afghanistan

Sama da mutane dari biyu ne suka mutu a wata girgizar kasa mai karfi wadda ta afkawa arewa, maso gabashin Afghanistan da kuma Pakistan.

Akasarin mace-macen a Pakistan ne, girgizar kasar ta fi kamari ne a kauyukan kasar masu tsaunuka da suke yankunan arewa.

A Afghanistan kuma a kalla 'yan makaranta 12 ne suka mutu a turmutsutsi a lokacin da suke kokarin fita daga cikin gine-gine.

Wasu rahotannin kuma sun ce girgizar kasar ta jawo zaftarewar kasa a yankuna masu tsaunuka na Pakistan wanda hakan zai baiwa masu kai agaji wahalar isa kauyukan.

Mazauna birnin Kabul sun ce ba su taba jin karar girgizar kasa irin wannan ba.

Kamfanonin sadarwa a kasar Afghanistan sun daina aiki, sannan asibitoci suna cikin shirin ko-ta-kwana.

Hukumar kula da yanayin kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar, wacce ke da karfin maki 7.5 a ma'aunin ricta, ta fi karfi a birnin Faizabad na Afghanistan da ke cike da tsaunuka.