NCC ta ci tarar MTN naira tiriliyan daya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption MTN na daya daga cikin kamfanonin sadarwa da suka fi suna a Nigeria

Hukumar da ke kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya, NCC ta ci kamfanin MTN tarar sama da Naira Tiriliyan daya.

An ci tarar kamfanin ne saboda gazawarsa wajen rufe layukan masu hulda da shi, wadanda ba su yi rijista ba har wa'adin yin rijistar ya wuce.

Wata sanarwa da MTN ya fitar ta tabbatar da cewa an ci tarar sa, sai dai ta kara da cewa kamfanin yana ci gaba da tattaunawa da NCC a kan rufe layukan wayoyin mutanen da ba su yi rijista ba.

Wannan shi ne karon farko da aka ci tarar wani kamfanin sadarwa makudan kudade saboda rashin bin umarnin hukumar.

Kamfanin na MTN dai ya yi kaurin-suna wajen rashin biyan bukatun masu hulda da shi.

Tuni dai darajar hannun jarin kamfanin na MTN a Afrika ta Kudu ta fadi da fiye da kashi biyar cikin 100, sakamakon rahotannin da ke cewar za a ci tarar kamfanin.

Alkaluma daga hukumar NCC sun nuna cewa akwai layukan wayar salula kusan miliyan 150 a Nigeria.