An nada sabon Ooni na Ife

Hakkin mallakar hoto Ooni Facebook Group
Image caption Sabon Ooni, Adeyeye Enitan Ogunwusi

Gwamnatin jihar Osun da ke kudancin Nigeria ta sanar da nadin sabon basaraken gargajiya, watau Ooni na Ife, Adeyeye Enitan Ogunwusi.

Yarima Adeyeye Enitan Ogunwusi shi ne aka zaba a matsayin Ooni na Ile-Ife na 51, wanda ya fito daga gidan sarautar Giesi.

Hakan na zuwa watanni uku bayan mutuwar tsohon basaraken, Oba Okunade Sijuwade a cikin watan Yuli a wani asibiti a London.

Sanarwar da gwamnatin jihar Osun ta fitar, ta ce nadin ya biyo bayan cika aikin da masu zaban Ooni suka yi cikin wadanda suka nuna sha'awar hawa kan karagar mulkin.

Sabon basaraken mai shekaru 40, an zabe shi ne daga cikin mutane 21 na gidan sarautar Giesi da aka kebe sarautar domin su.

Bisa al'ada Ooni na Ife, yana daga cikin zuri'ar ubangijin gargajiya na kabilar yarabawa watau Oduduwa.