Ana gallaza ma ni a kurkuku - Saadi Gaddafi

Hakkin mallakar hoto .
Image caption 'Ya'yan Gaddafi na tsaka mai wuya a Libya

Daya daga cikin 'ya'yan tsohon shugaban Libya, Muammar Gaddafi ya shaida wa wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama cewar ana gallaza masa a cikin kurkuku.

Saadi Gaddafi wanda ake tsare da shi a wani gidan yari da ke Tripoli, ana sa ran a mako mai zuwa zai bayyana a gaban kuliya.

Saadi ya bayyanawa tawagar kungiyar Human Rights Watch da ta ziyarce shi a watan da ya gabata, cewar an kebe shi a kurkuku ba ya mu'amala da kowanne fursuna.

Ya kara da cewar ana matsawa shaidunsa lamba sosai a Libya.

A watan Agusta ne aka fitar da wani bidiyo wanda ke nuna wasu gandirebobi na cin zalin Saadi Gaddafi.