An dage shari'ar Sambo Dasuki

Image caption Sambo Dasuki ya musanta zargin da ake yi masa.

Wata babbar kotun Abuja a Najeriya ta dage shari'ar da take yi wa Kanar Sambo Dasuki saboda zargin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Kotun ta ce za ta ci gaba da gudanar da shari'ar ranar Laraba.

A ranar daya ga watan Satumba ne alkalin kotun, Ademola Adeniyi, ya bayar da belin tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara a kan tsaro bisa "lura da kimar sa" ta kasancewa daya daga cikin mutanen da suka bautawa Najeriya.

Gabanin bayar da belin nasa, lauyan gwamnatin tarayya, Mohammed Diri, ya shaida wa kotun cewa sun gurfanar da shi a gaban ta ne bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Sai dai Kanar Dasuki ya musanta zargin da ake yi masa.

Daurin shekaru goma

Lauyan gwamnatin ya ce hukumar tsaron farin-kaya ta kasar ta je gidan Kanar Dasuki a watan Yuli, inda ta same shi da makamai.

Ya kara da cewa hakan zai iya sanya wa a daure shi a karkashin dokokin Najeriya.

Lauyansa, J.B. Daudu, ya bukaci kotun ta bayar da belinsa, kuma masu shigar da kara ba su nuna kin amincewa da bukatarsa ba.

Sai dai alkalin ya bukaci a kwace fasgo din Kanar Dasuki, a ajiye a kotun domin kada ya fice daga kasar.

Kanar Dasuki shi ne babban jami'in gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da aka gurfanar a gaban kotu ya zuwa yanzu.

Idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar daurin shekaru goma a gidan yari.