Boko Haram: Rashin tabbas a Borno ?

Hakkin mallakar hoto Screen Grab
Image caption 'Yan Boko Haram sun ce sunanan daram

Ana samu rahotanni masu cin karo da juna kan batun wuraren da har yanzu ke ƙarƙashin ikon ƙungiyar Boko Haram a jihar Borno.

An ambato gwamna Kashim Shettima na cewa ƙananan hukumomin Abadam da Mobbar, da kuma wani bangare na ƙaramar hukumar Marte ne ke karkashin ikon Boko Haram.

Amma shi kuma babban hafsan sojojin kasar, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya musanta hakan, inda ya ce babu ko da gari daya a ƙarƙashin ikon Boko Haram a jihar Borno

Wani dan asalin Ababam ya shaidawa BBC cewa fiye da shekaru guda kenan da al'umma Abadam suka bar garin sannan a cewarsa babu jami'an tsaro a garin.

"Abadan dai indai maganar gaskiya ce ba mutane a Abadam duk suna can a tsallaken Nijar, da mahaifina, da mahaifiya ta duk suna can a tsallaken Nijar," in ji mutumin.

Image caption Gwamna Shettima ya fasa 'kwai'

Ya kara da cewa "Saboda su (iyaye na) na tsoron rayuwarsu, kar a kashe su, domin 'yan Boko Haram sun zo sun ce a bar masu gari, sama da shekara daya yanzu suna can."

Da aka tambaye shi ko sojojin Najeriya suna shawagi ne a wurin?, sai ya ce "Babu sojoji ba su ƙarasa can ba, tun bara ne sojojin Chadi da suka zo suka fatattaki yaran, sojojin Chadi din kuma suka janye suka koma, a yau da nake maka magana sojoji ba su sake komawa nan ba, ƙarshen su dai Kukawa da Baga."

Sai dai BBC ba ta da wata hanyar tabbatar da ikirarin gwamna Shettima ko sojojin Nigeria, ko kuma wasu daga cikin 'yan jihar Borno da aka zanta da su.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 20,000 tare da raba wasu miliyoyi daga muhallansu.

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army
Image caption Janar Buratai ya musanta zargin da gwamna ya yi