Aikin ceto kan girgizar kasar Afghanistan da Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ma'aikatan ceto na kokarin shiga yankunan da ke cike da tsaunuka.

Masu aikin ceto na ci gaba da yunkurin isa wurare masu wahalar shiga domin taimakawa mutanen da girgizar kasa ta afkawa a kasashen Afghanistan da Pakistan.

Girgizar kasar-- mai karfin maki 7.5 a ma'aunin ricta --ta yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 300, yayin da mutane 2,000 suka samu raunuka.

An aika da ma'aikatan ceto zuwa ga yankuna masu cike da tsaunuka saboda har yanzu ba a san girman matsalar a can ba.

Wasu mata 'yan makaranta 12 a Afghanistan na cikin mutanen da suka mutu a lokacin da suke kokawar ficewa daga azuzuwansu domin tserewa girgizar kasar.

Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani, wanda ya yi jawabi ga 'yan kasar ta gidan talabijin, ya bukaci mutanen da ke zaune a yankunan da girgizar kasar ta shafa da su taimakawa masu aikin ceton.