Amurka za ta zafafa kai hare-hare kan IS

Image caption Sakataren tsaron Amurka Ash Carter

Sakataren tsaron Amurka Ash Carter ya ce za a samu sauyi a kan dabarun da kasarsa ke amfani da su wajen yaki da kungiyar IS a Iraki da Syria.

Da yake jawabi a gaban kwamitin tsaro na majalisar dattijan kasar, Mr Carter ya ce hadakar dakarun da Amurka ke jagoranta masu yaki da kungiyar za su zafafa luguden wuta ta sama, sannan za a iya samun karuwar amfani da karfi ta kasa kan mayakan na IS.

Ya kara da cewa sun yanke shawarar ci gaba da taimaka wa 'yan tawaye da ke yaki da kungiyar ta IS a yankin Raqqa da kayan yaki.

A cewar sa, dakarun kawancen ba za su ja da baya ba wajen yaki da kungiyar ta kasa.

A makon jiya, sojojin Amurka -- tare da gudunmuwar mayakan Kurdawa -- sun kubutar da wasu fursunoni da mayakan IS ke tsare da su a arewacin Iraki.