An amince shugaban Congo ya yi ta-zarce

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Sassou Nguesso ya fara mulki a shekarar 1979.

A Congo, sakamakon kuri'ar raba-gardamar da aka yi ya nuna cewa 'yan kasar fiye da kashi 90 cikin dari sun amince shugaba Denis Sassou Nguesso ya tsaya takara a karo na uku.

A karkashin kundin tsarin mulkin kasar, shugaban ba shi da damar sake tsayawa takara saboda ya haura shekara 70 a duniya, kuma ya yi mulki sau biyu.

'Yan hamayya sun ce rashin fitowar mutane a lokacin kada kuri'ar raba-gardamar ya isa ya sa a soke zaben.

Sai dai alkaluman da hukumomi suka fitar sun nuna cewa mutane fiye da kashi 72 cikin dari ne suka kada kuri'unsu a zaben da aka yi ranar Lahadi.

Hukumar zaben kasar ta ce fiye da mutane miliyan daya da dubu 200 (1.2 m) ne suka amince a gyara kundin tsarin mulkin, yayin da mutane kusan 102,000 suka yi watsi da sauyin.

'Yan hamayya sun yi kira da a kaurace wa zaben, kuma daya daga cikin shugabanninsu ya bayyana zaben a matsayin mai cike da magudi.

Shugaba Sassou Nguesso, mai shekaru 71, na daya daga cikin shugabannin Afirka da suka fi dadewa a kan mulki, inda ya fara mulki a shekarar 1979 zuwa 1992 lokacin da ya sha kaye a zaben da aka yi.

Shugaban ya sake hawa kan mulki a shekarar 1997 bayan wani yakin basasa da bai dade ba, kuma tun daga lokacin ya sake cin zabe sau biyu.

Yanzu yana dab da kammala wa'adinsa na biyu na shekaru bakwai.