Me ya sa ake jinkirin sanar da sakamakon zabe a Afrika?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana gudanar da Shirye-shiryen zabe

Ranar Lahadi da ta wuce ta kasance ranar da ake yin zabuka a kasashe da dama a duniya. A cikin 'yan sa'o'i an sanar da sakamakon zaben kasashen Argentina da Guatemala da kuma Poland, amma mahukunta a Tanzania da Ivory Coast sun ce sakamakon zaben da aka yi a kasashen zai dauki kwanaki kafin ya fito.

Mutane da dama dai ba sa jin dadi dangane da yadda ake gudanar da harkokin zabe.

Ba wai masu kada kuri'a ne ko 'yan takara ba ne ke kaguwa su ji sakamakon zaben.

Su kansu jami'an zaben wadanda suka hana idanun su bacci, suna kuma aiki ba dare ba rana, ba sa hutawa domin ganin an yi komai lafiya, suma suna son ganin komai ya tafi dai-dai.

A Kinshasa babban birnin jamhuriyar dimokradiyyar Congo a shekarar 2011, a iya tunawa malaman zabe sun kwanta a kan tabarma a cibiyoyin zabe a kan takardun kada kuri'a.

Kazalika a wannan shekarar ma dai a Najeriya na kalli na ga kwamishinan zaben jihar Edo idanuwansa sun yi Ja ga shi ya gaji likis yana jiran sakamakon zabe na karshe wanda za a kawo bayan an hau hau jirgin ruwan domin tattara kan alkaluma.

Sakamakon zaben Shugaban kasa na tafiyar hawainiya sosai a Afrika

Matsalar ba ta rashin kayan aiki ba ce

Har yanzu Biritaniya na amfani da tsohon tsarin zabe, saboda haka ana gudanar da zabe a kowacce mazaba yadda ya kamata kuma ana sanar da sakamakon zaben nan take; ba bu bukatar jiran sakamakon zabe daga ko ina a kasar, kuma nan take ake sanin waye zai kasance Firai minista na gaba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu kada kuri'a na fargabar magudi a zaben da suka kada kuri'un su

'Fargabar magudin zabe'

Wani abin ban sha'awa da zaben Biritaniya shi ne akwai gaskiya.

Idan aka samu dan magudi kadan, ba bu bukatar daukar wani dogon lokaci, nan da nan ake magance komai ba bata lokaci.

Jami'an zabe a cibiyoyin zabe za su kira waya su sanar da sanar da sakamakon zaben cibiyar su, kuma ba bu wanda zai zarge su akan wani magudi. Sai dai kuma ba haka abin ya ke ba Afrika.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Malaman zabe sun tattara sakamakon zabe

A wasu lokuta sakamakon zaben da ake kai wa ba shi ne na ainihi ba ne a Afrika.

A jamhuriyar dimokradiyyar Congo, kungiyar tarayyar Turai ta lura cewa sakamakon zaben da ta sanya ido a lardin Katanga bai yi dai-dai da wanda aka bayyana ba.

Shi ne dalilin da ya sa malaman zaben ke kwanciya a kan takardun kada kuri'a.

Duk kokarin da ake na amfani da na'urorin zamani a yayin gudanar da zabe bai samu nasara ba sosai.

A gaskiya akwai kalubale a bangaren kayayyakin aiki a Afrika, kuma hanyoyin sadarwa ba su da tabbas, saboda haka akwai bukatar a rubanya kare kayayyakin zabe domin a samu sahihin sakamako.

Amma kuma ba za a cimma hakan ba, har sai kowa ya yarda cewa akwai hanya mafi sauki, da masu kada kuri'a a Afrika za su bi, domin idan ba haka ba to sai sun yi jira mai tsawo kafin su ga sakamakon zabe.