Ministan Indiya ya soki 'yan sanda kan nama

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An hana cin naman Shanu a India

Ministan babban kasar India Delhi ya soki 'yan sanda akan abin da ya kira luguden wutar da aka yi akan wani gidan gwamnati na musamman saboda ana zargin cewa ana raba nama a gidan.

Daruruwan 'yan sanda ne suka shiga gidan da ake cewa Kerala wanda mallakar kudancin kasar ta India ne.

Sai dai kuma 'yan sandan sun kare matakin da suka dauka inda suka ce sun samu rahoton cewa ana cin naman Saniya a gidan.

Kuma an haramta cin naman Delhi.

Ma'aikatan gidan sun ce ko shakka babu suna raba naman Saniya, amma kuma sun amince za su cire shi daga cikin jerin abincin da ake ci a gidan.