Yoyon fitsari na karuwa a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters

Masana harkar lafiya a Najeriya sun nuna damuwa game da yawan karuwar cutar yoyon fitsari a tsakanin matan kasar.

Masana sun ce a duk shekara ana samun mata wadanda suke kamuwa da cutar dubu 12, amma dubu biyar ne kawai ake iya yi wa magani.

Kwararrun sun bayyana haka ne a wajen wani taro da shirin Fistula Care da ke karkashin hukumar tallafawa kasashen duniya ta Amurka wato USAID ta shirya a Kano kan matsalar ta yoyon fitsari.

Wani kwararren likitan mata a Kano Dr. Habibu Sadauki ya shaidawa BBC cewa a Nigeria mata dubu 150 zuwa dubu 200 ne wadanda ke fama da wannan cutar.

Likitan ya kuma ba da shawarar zuwa asibiti a lokacin haihuwa.