Walmart na shirin amfani da jirgi maras matuki

Hakkin mallakar hoto Getty

Katafaren kamfanin saida kayayyaki na Walmart, wanda shi ne yake mallakar Asda a Biritaniya ya nemi izinin soma gwajin jirage marasa matuki masu kai kaya a Amurka.

Kamfanin ya nemi hukumar kula da sararin samaniya ta FAA a kan ko zai iya soma gwajin jiragen marasa matuki wajen kai kayayyakin da aka saya daga kamfanin zuwa gidajen mutane da kuma manyan wuraren adana kaya

Walmart shi ne kamfanin saida kayayyaki mafi girma a duniya ta fuskar riba, kuma yana bin sawun kamfanin Amazon, wanda tuni yake gwajin jiragensa marasa matuki saboda wannan dalili

Ta bayyana cewa tuni Walmart ya soma gwajin irin wadannan jirage a cikin gida

Za a kebe wasu ayyuka da jiragen za su rinka yi da suka hada da ajjiye kaya a wuraren da ake ajiye motoci na kamfanin Walmart domin kwastomomi su kwasa da kuma bincike a manyan wuraren ajjiye kayayyaki na kamfanin

Idan har hukumar FAA ta bai wa kamfanin izini, Walmart na shirye shiryen amfani da wadannan jirage marasa matuki da kamfanin China na DJI ya kera

Tunda farkon wannan shekarar, kamfanin Amazon ya sami izinin soma gwajin wadannan jirage a waje, kodayake sai ya bi dokoki da aka tanadar masa

Kamfanoni da dama sun soma binciken yiwuwar amfani da jirgi maras matuki wajen kai kaya da suka hada da kamfanin China na Alibaba da kamfanin aike da wasiku na DHL