Sojoji na neman 'yan Boko Haram 100 ruwa a jallo

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption Daya daga cikin mayakan Boko Haram

Rundunar sojin Nigeria ta ayyana wasu mayaka kungiyar Boko Haram su 100 a matsayin wadanda take nema ruwa-a-jallo.

Babban hafsan sojin kasar, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai a yayin wani taro a Maiduguri babban birnin jihar Borno, ya kuma kaddamar da fasta wacce ke dauke da hotunan wadanda take neman ciki har da shugaban kungiyar Abubakar Shekau.

Fasta din na dauke da rubutu a harsuna daban-daban na Nigeria da kuma lambobin da jama'a za su iya kira idan suna da bayanai kan 'yan Boko Haram din su 100.

Kakakin rundunar sojin, Kanar Sani Usman Kukasheka ya shaidawa BBC cewar hotunan na dauke ne da huskokin 'yan Boko Haram din da suke tafka ta'asa.

"An sa hotunansu a wata sanarwa kunshe da bayanai a harshen Ingilishi da Hausa da kuma Kanuri kuma ko wacce fuska akwai lamba a jiki," in ji Kukasheka.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane kusan 20,000 a yayin da wasu miliyoyi suka fice daga muhallansu.

Lambobin wayar tarho da rundunar ta bayar su ne; 08181555888, 08160030300, 07053333123