An wanke daya daga cikin alkalan Ghana

Image caption Mai shari'a Georgina ce ta wanke alkalin

Babbar mai shari'a ta kasar Ghana ta wanke daya daga cikin alkalai bakwai da aka dakatar daga aiki a kan zarge-zangen cin hanci.

Babbar mai shari'ar, Georgina Theodora Wood, ta ce hukumar gudanar da bincike ta Tigeyere PI ba ta bada isassun shaidu ba da ke nuna cewa mai shari'a Asmah Akwasi Asiedu ya karbi cin hanci lokacin da ya ke alkalin wata karamar kotu.

Anas Armaya'u Anas, wani dan jarida da ya yi bincike a boye ne ya jagoranci hukumar ta Tigeyere PI, kuma ya kwashe shekaru biyu yana gudanar da bincike a kan zargin cin hanci a bangaren shari'ar kasar Ghana.

Ya dai mika bidiyo kusan na tsawon sa'o'i dari biyar a matsayin wata shaida a kan alkalai sama da talatin da jami'an kotu kusan dari biyu.