Dokar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Kaduna

Image caption Gwamna Nasir Elrufai na kokarin kawar da miyagun mutane a jihar

Gwamnatin jihar Kaduna a arewacin Najeriya ta amince da wani kudurin doka ta hana shaye-shaye da kuma cinikayyar miyagun kwayoyi a jihar.

Dokar wacce ma'aikatar shari'a ta jihar ta tsara, tuni ta sami amincewa da kuma gamsuwar majalisar zartarwa ta jihar.

Hakan wani mataki ne a kokarin dakile shaye-shaye musamman tsakanin matasa da gwamna Nasir ElRufai ya sha alwashin yi.

Shayen miyagun kwayoyi dai a yanzu wata babbar matsala ce a arewacin Najeriya kuma jama'a da dama na ganin matsalar karancin ayyukan yi da talauci ne ke kara ingiza matasa shiga cikin shaye- shaye.

A yayin da gwamnati ke kokarin kafa wannan doka dai, wasu matasa na cewa a hada da samar musu da ayyukan yi domin a samu nasarar yaki da shan miyagun kwayoyi a jihar.