Zakuna na fuskantar barazanar karewa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zakuna suna hutawa

Wani sabon bincike da aka yi ya nuna cewa akwai yiwuwar za a iya samun raguwar zakuna da kusan rabin adadinsu a nahiyar Afrika a cikin shekara 20 saboda farautarsu da ake yi da kuma bukatar da jama'a ke nunawa ta nome dazuka.

Binciken da aka shafe shekara 20 ana yi wanda wata cibiyar kimiyya a Amurka ta wallafa ya bayyana cewa nan gaba zakunan za su kasance saura dubu 20 ne kawai a nahiyar Afrika.

Sai dai kuma zakunan ba za su yi karanci ba a kasashen Botswana da Namibia da Africa ta kudu da kuma Zimbabwe saboda ana samun karuwarsu a kasashen.

Masu binciken sun yi kididdigar cewa a tsakiyar karni na 20 an samu karuwar Zakuna inda suka kai dubu 200 a Afrika.

Yawanci zakunan sun gudu ko kuma ba a san inda suke ba. Yanayin ya baci a Afrika kamar yadda binciken ya nuna saboda barazanar