Marks & Spencer ya samu matsala da shafinsa na Intanet

Hakkin mallakar hoto PA

Matsalar shafin Intanet da kantin Marks and Spencer ya gamu da ita ya bai wa kwastomomi damar ganin bayanan junansu.

Kantin sayar da kayayyakin ya dakatar da shafin nasa na intanet har tsawon sa'oi biyu a ranar Talata da daddare domin gyara matsalar.

Kantin ya ce matsalar sakamakon wani kuskure ne da aka samu a cikin gida ba kutse ba.

Ya kara da cewa cikakkun bayanan katinan sayayyar kwastomomi ba sa cikin bayanan da suka fita.

Sai dai an ga bayanan mutane da suka hada da sunaye da ranar haihuwa da lambar waya.

Marks and Spencer ya nemi afuwar wannan matsala da aka samu.

Ba a dai san takamaimai bayanan yawan mutanen da wasu kwastomomin Marks & Spencer suka gani ba sakamakon wannan matsala.