An kammala tantance ministocin Nigeria

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption Rotimi Amaechi a lokacin da ya ke jawabi ga majalisa

Majalisar dattawan Nigeria ta kammala tantance sunayen mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ya aika mata domin nada a matsayin ministoci a kasar.

Shugaban majalisar, Sanata Abubakar Bukola Saraki wanda ya jagoranci zaman na ranar Laraba, ya karanto sunaye mutane biyar da aka tantance a zauren majalisar.

Mutane biyar din da aka tantance wadanda su ne ciko na karshe da suka rage daga cikin mutanen da shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar sun hada da Mr Okechukwu Enyinam Enelamah da kuma Mohammed Musa Bello.

Sauran su ne Malam Adamu Adamu da Aisha Abubakar da kuma Nwoka Anthony.

A yanzu abin da ya rage shi ne a ranar Alhamis, majalisar dattawan ta amince da mutane 18 da ta tantance domin bai wa shugaba Buhari damar rantsar da su a matsayin ministoci.

A 'yan makonnin da suke wuce majalisar dattawan ta tantance ta amince da mutane 18 daga zubin farko da shugaban kasar ya aike mata.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption Wasu daga cikin wadanda majalisa ta amince da su

Wadanda aka riga aka amince da su bayan tantance su, sun hada da tsohon gwamnan jihar Lagos, Babatunde Raji Fashola da Kayode Fayemi da Laftar Janar AbdulRahman Dambazau da Alhaji Lai Muhammed da Hajiya Amina Mohammed da kuma Barrister Solomon Dalung.