Wacece Amaryar Adam Zango?

Hakkin mallakar hoto Adam Zango
Image caption Oummoul Koulsoumi haifaffiyar Ngaoundere ce a Kamaru.

Ana ci gaba da samun karin bayani game da amaryar jarumin fina-finan Hausa Adam Zango, mai suna Oummoul Koulsoumi Yaya.

Oummoul Koulsoumi, haifaffiyar birnin Ngaoundere ce a Kamaru, kuma mahaifinta shi ne marigayi Yaya Bello wanda kanin sarkin zangon Beka ne da ke karamar hukumar Ngaoundere ta farko.

Baya ga haka kuma, tana da alaka da gidan sarautar birnin Ngaoundere ta fannin auratayya.

Wasu majiyoyi daga Kamaru sun shaida wa BBC cewa akwai dadaddiyar alaka a tsakaninta da mai gidanta Adam A. Zango.

Bayanan sun nuna cewa Adam Zango ya gamu da amaryar tasa ne, ta hanyar wani dan uwansa da ya aika Ngaoundere wurin wani babban attajirin birnin, mai suna Alhadji Abbo Ousmanou dauke da fefen wakar da ya raira masa.

Oummoul Koulsoumi ta kasance daya daga cikin tawagar 'yan matan da suka tarbi bakon na Alhadji Abbo a filin jirgin sama na Ngaoundere.

Bayanan sun nuna cewa, Oummoul Koulsoumi ta bada sako a kai wa Adam Zango, daga nan aka fara samun musayar sakwanni tsakaninsu, hakan kuma ya kai ga daura masu aure.

Oummoul Koulsoumi ta fara makarantar sakandare, amma bata kammala ba.