An soke dokar haihuwar ɗa ɗaya a China

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kaddamar da dokar haihuwar da daya ne a shekarar 1979 domin rage yawan al'ummar kasar.

Kasar China ta yanke shawarar daina amfani da dokar nan da ta amince ɗa ɗaya kawai ma'aurata za su rika haifa.

Kamfanin dillancin labaran kasar, Xinhua, ya ambato jam'iyyar Kwaminis na cewa daga yanzu an amince ma'aurata su rika haifar 'ya'ya biyu.

An kaddamar da dokar haihuwar da guda din mai cike da cece-kuce ne a shekarar 1979 domin rage yawan mutane a kasar.

Sai dai hakan ya sa kasar na fama da karancin matasa a yayin da tsofaffi ke ci gaba da mutuwa.