An kai wa 'yan adawa hari a Myanmar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aung San Suu Kyi na fuskantar matsin lamba

Maza dauke da wukake sun kai hari a kan ayarin gangamin yakin neman zabe na babbar jam'iyyar adawa ta National League for Democracy-NLD a birnin Yangon na Myanmar.

Dan takarar jam'iyyar NLD a yankin an garzaya da shi zuwa asibiti saboda ya ji rauni a kansa da hannuwansa.

Bayanai sun ce a yanzu haka magoya bayan jam'iyyar NLD sun kewaye asibitin.

Harin na zuwa ne, kwanaki goma kafin gudanar da babban zabe a Myanmar wanda shi ne karon farko cikin shekaru 25 da zai kasance zabe a bude.

Nan da kwanaki uku ne, ake sa ran shugaban jam'iyyar NLD, Aung San Suu Kyi za ta yi gangami a birnin na Yangon.