Majalisa ta amince da nadin shugaban INEC

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Farfesa Yakubu ya ce ba zai yarda da magudin zabe ba

Majalisar dattawan Nigeria ta amince da nadin Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar zaben kasar, INEC.

A zaman majalisar karkashin jagorancin Sanata Abubakar Bukola Saraki, an yi wa Farfesa Yakubu tambayoyi a kan yadda zai ja ragamar harkokin zaben kasar.

Da yake amsa tambayoyin, Farfesa Yakubu ya ce zai yi adalci wajen gudanar da zabe a kasar ba tare da son zuciya ba.

Majalisar kuma ta amince da nadin wasu kwamishinoni biyar na INEC watau Dr. Anthonia Okoosi Simbine da Alhaji Baba Shettima Arfo da Amina Zakari Mohammed da Mustapha Lecky da kuma Soyebi Solomon.

A makon jiya ne shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisa sunan Farfesa Yakubu domin ta amince da shi a matsayin shugaban INEC.