Kwastam ta yi wa jami'anta 34 ritaya

Kanal Ali ya sha alwashin yi wa hukumar Kwastam garanbawul.

Asalin hoton, Nigeria Custom

Bayanan hoto,

Kanal Ali ya sha alwashin yi wa hukumar Kwastam garanbawul.

Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, watau Custom ta yi wa manyan jami'anta 34 ritaya daga aiki.

Hukumar, wacce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar, ta ce ta dauki matakin ne domin yin sauye-sauye a cikinta, kamar yadda sabon shugabanta, Kanar Hameed Ali (mai Ritaya), ya sha alwashin yi.

Sai dai gabanin sallamar manyan jami'an nata, biyar daga cikin su sun mika takardunsu na yin murabus daga kan mukamansu.

Mutanen su ne: John Atte, Ibrahim Mera, Musa Tahir, Austin Nwosu da Akinade Adewuyi.

Yawancin jami'an da suka yi murabus suna da mukaman mataimakan shugaban hukumar.

Hukumar ta yi kaurin-suna wajen karbar hanci da rashawa.

Bayanai sun ce gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta sha alwashin kawar da cuwa-cuwa a hukumar kwastam ta kasar.