Amurka za ta tura dakaru zuwa Syria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A yanzu haka akwai jiragen yakin Amurka da ke yaki a Syria

Amurka za ta tura dakaru na musamman guda 50 zuwa arewacin Syria domin bada shawara ta fuskar soji a yaki da kungiyar IS.

A nan gaba ne, fadar Amurka za ta yi karin haske kan yadda za ta tura dakarun.

A yanzu haka dai akwai wasu dakarun Amurkar wadanda ke yaki da kungiyar ta IS a Syria.

Sai dai ta sama ne kawai Amurka a yanzu take yaki da mayakan IS watau da jiragen yaki kuma babu tabbaci a kan ko za a tura dakarun sojin kasa.

A waje daya kuma, rahotanni daga Syria sun ce akalla mutane 40 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikata sakamakon hari ba kakkautawa da dakarun gwamnati suka kai a Douma, wani gari da ke hannun 'yan tawaye a kusa da Damascus.

Kungiyar masu sa ido kan hakkin dan adam ta Syria watau, Syrian Observatory for Human Rights ta ce an harba makaman roka a kan wata kasuwa.

Ta ce mutane sun makale cikin baraguzan gine-gine.