Duniya na fuskantar matsanancin halin rayuwa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A taron manema labarai shugaban kungiyar agaji ta Red Cross na duniya Mr Maurer ya yi kakkausar suka akan yadda shugabannin duniya suka kau da kai ga mummunan tasirin da yake yake ke haifarwa ga rayuwar al'ummar duniya

Yace an shiga wani sabon karni wanda ba mai kwanciyar hankali ba ne. Yawaitar dauki ba dadi da makamai sun tsunduma duniya cikin halin yaki.

Ban Ki Moon da shugaban kungiyar agaji ta Red Cross na duniya Peter Maurer suka ce duniya na fuskantar matsanancin halin rayuwa da rashin kwanciyar hankali.

Sun yi kira a dauki ingantattun matakai domin saukaka wahaloli da jama'a fararen hula suke fama da su.

Musamman sun bukaci daukar mataki a kan kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai a kuma hukunta su bisa ta'asar da suka aikata.

Hakan nan kuma sun bukaci a kawo karshen amfani da manyaman makamai a wuraren da jama'a ke zaune.