Fada: Kotu ta takawa Sarkin Kano birki

Hakkin mallakar hoto Getty

Wata kotu a Kano ta umarci Sarkin Kano da kuma majalisar masarautar Kano din su dakatar da shirin korar wasu dake zaune a cikin fadar da ake kira Gidan Rumfa har sai an gama sauraron karar da aka shigar akan batun.

Dan uwan sarkin Kanon mai suna Salim Bayero ne ya shigar da kara gaban kotu yana kalubalantar shirin Sarkin Kanon daga yunkurin rushe wani wuri dake da kaburran sarakunan Kanon 13 domin ginawa hakimai ofisoshi.

Wanda ya shigar da karar ya nemi kotu ta kuma hana Sarkin Kanon Muhammadu Sanusi II korar wasu mutane dake zaune a wani bangaren fadar da ake shirin rushewa.

Yanzu dai kotu ta sanya ranar 12 ga watan Nuwamba domin ci gaba da sauraron karar

A baya baya nan masarautar Kano ta fuskanci wani rikicin na cikin gida inda aka tube babban dan marigayi Sarki, Ado Bayero, wato Lamido Ado Bayero daga matsayin Ciroman Kano bisa zargin rashin yin mubayi'a ga Sarki.