Majalisar wakilai za ta dauki mataki kan Burtaniya

Majalisar dokokin Najeriya Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

Majalisar Wakilai ta tarayyar Najeriya ta ce za ta sanya baki cikin maganar maido da 'yan Najeriya kimanin dubu 49 da gwamnatin Biritaniya ke shirin yi bisa zargin rashin mallakar iznin zama a kasar.

An dai dorawa wa kwamitocin al'amuran kasashen waje da wanda ke sanya ido kan 'yan Najeriya da ke zaune a kasashen ketare, alhakin shiga cikin lamarin.

Jakadan Najeriya a Biritaniya shi ne ya shaida wa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, lokacin da ya kai ziyara London, cewa hukumomin Birtaniya na shirin dawo da 'yan Najeriyar gida.

Ya ce da yawan wadanda ake shirin dawo da su din sun shafe shekaru da dama a Biritaniya ba tare da sun zo gida Najeriya ba.