'Yan sandan Najeriya suna cikin tsaka-mai-wuya'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'yan sandan Najeriya

Wasu 'yan sanda da suka tattauna da BBC kan yanayin da aikin dan sanda a Najeriya yake ciki sun ce suna cikin halin ni-'yasu.

Wani daga cikin 'yan sanda ya shaida wa bbc cewa cin hanci da rashawa wani abu ne da ya zama dole ga dan sanda idan har yana son ya rayu bisa la'akari da kudin da ake ba su a matsayin albashin wata wadanda ba su taka kara sun karya ba.

Ya ce " kurtu mara igiya yana karbar dubu 42, kofur mai igiya biyu kuma yana daukar 43, a inda shi kuma sajan yake karbar 44, insipeta ne yake karbar dubu 67 zuwa 70".

Dan sanda wanda ya nemi a sakaya sunansa ya kara da cewa hakan ne yake sa 'yan sanda karbar na goro a bakin aikinsu, kuma ba a aika mutum wurin da zai karbi hasafin har sai ya amince zai kawo wa oganninsa nasu kason.

Dangane kuma da yanayin makwanci da kayan aiki, 'yan sanda sun ce ana ba su harsashi guda uku domin tunkarar 'yan fashi da makami sannan kuma idan dan sanda ya mutu a wurin aiki tambayar da manyan za su fara yi, ita ce ina bindiga?

Batun makwanci kuwa dan sandan ya ce abun ba a cewa komai domin a cewarsa akan iya gwamutsa mutane fiye da biyar a daki daya musamman samari.