Gobara ta kashe mutane 27 a Romania

Motocin daukar marasa lafiya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Motocin daukar marasa lafiya a wajen wurin da lamarin ya faru

Akalla mutane 27 ne suka rasa ransu sannan sama da dari da hamsin suka jikkata sakamakon wata wuta da ta tashi a wani gidan rawa da ke Bukarist, babban birnin kasar Romania.

Daruruwan mutane ne suka yi dandazo domin kallon rawa a lokacin da wutar ta tashi, al'amarin da ya haifar da turmutsutsi wajen neman kofar fita domin tsira da rai.

wani wanda abin ya faru a kan idanunsa ya shaida wa bbc cewa mutane sun ta bi ta kan juna domin neman tsira sannan wasu sukai ta suma saboda hayakin da suka shaka.

Shugaba Klaus Lohanis na kasar Romania ya ce lamarin ya tayar masa da hankali kuma ya bayana ranar a matsayin rana ce ta bakin ciki ga kasar baki daya.