Gobara ta tashi a gidan rawa a Romania

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an agaji na aikin ceto a gidan rawa a Romania

Shugaban kasar Romaniya Klaus lohannis ya ce an yi watsi da ka'idojin kiyaye hadura a wani gidan rawa da ke Bucharest in da mutane ashirin da bakwai suka rasa rayukansu a daren ranar jumma'a.

Wadanda suka tsira da ransu sun ce gobara ce ta tashi sakamakon wasan wuta da akeyi a wajen.

Mutanen sun ce an samu turmutsutsu a hanyar da ake fita da ga gidan rawar, inda mafi da yawa daga cikin wadanda suke a ciki hayaki ya fara tagayyarasu.

Likitoci na kokarin ceto rayukan wadanda suka kone yayinda mahukunta kuma ke cewa akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa.

Har yanzu akwai mutane fiye da dari da arba'in a asibiti suna karbar magani.