Saudiyya: Yakin Yemen ya kusa zuwa karshe

Adel Jubair Ministan harkokin wajen Saudiyya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Adel Jubair Ministan harkokin wajen Saudiyya

Adel Jubair ya shaidawa wani taro kan al'amuran tsaro a Bahrain cewa ana iya cimma yarjejeniyar sulhu da 'yan tawayen Houthi.

Kasar Saudiyya dai ta na marawa gwamnatin Yemen baya kuma a yanzu ta na jagorantar kawancen hadin gwiwa wajen yaki da yan Houthi.

Da yake bayani game da tattaunawar da aka yi ranar Juma'a a Geneva domin kawo karshen yakin Syria, Mr Jubair yace akwai batutuwa biyu, makomar shugaba Bashar al-Assad da kuma lokacin ficewar sojojin kasashen waje dake cikin Syria musamman sojojin Iran.